Connect with us

News

An kama ɗan Chinan da ke tozarta yaran Afirka a bidiyo

Published

on

Daga Usman Abdullahi jibirin

An kama ɗan Chinan da hukumomin Malawi ke nema ruwa a jallo wanda ake zarginsa da ɗaukar bidiyon yaran Afirka yana tozarta su.

An kama mutumin mai suna Lu Ke ne a ƙasar Zambiya mai maƙwabtaka da Malawi a ranar Litinin.

Lu Ke mazaunin Malawi ne da wani binciken BBC Afira Eye ya bankado shi inda yake amfani da yaran Malawi a bidiyo yana saka su suna zagin kansu a matsayin su na baƙaƙe ƴan Afirka.

A kan sayi ire-irien bidiyon da mutumin ke yi a kan dala 70 a shafukan sada zumunta a China.

Lu Ke dai ya yi watsi da zargin cewa yana amfani da kalaman muzantawa inda ya ce yana bidiyonsa ne on yaɗa al’adun China, don haka ba zai yarda a yi masa shari’a ba.

Advertisement

Mai magana da hukumar shige da fice ta Malawi Pasqually Zulu ya ce a halin yanzu Malawi da Zambiya na ƙoƙrin ganin an mayar da ɗan Chinan Malawi don a ci gaba da bincike.

Me ya faru tun farko?

A watan Fabarairun 2020 ne wani bidiyo mai kiɗimarwa ya fara karaɗe dandalin sada zumunta na China.

Wata murya da ba a gani na umartar wani rukukuni na yaran Afirka su faɗi wasu jimloli da harshen Chinanci.

Yaran na maimata kalaman cikin nishaɗi – amma ba su san cewa abin da ake faɗa musu yana nufin “ni dodo ne kuma ba na fahimta” ba. Bidiyon ya jawo ɓacin rai a China da wajen ƙasar.

Sai dai babu wanda ya taɓa ba da amsoshin: Me ya sa aka ɗauki bidiyon? A ina aka ɗauke shi? Wane ne ya ɗauke shi?

Advertisement

Wakilan sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, Runako Celina da Henry Mhango, sun yi balaguro har zuwa inda ‘yan China ke gudanar da ayyukan tozarta yaran don samun kuɗi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending