Connect with us

News

Gwamnan Ondo ya bayar da umarnin saka kemara a duka wuraren ibada a jihar

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya saka hannu kan wata doka da za ta tilasta saka kemarori a duka wurin taron jama’a da wurare masu zaman kansu a Jihar Ondo.

Advertisement

Gwamnan Akeredolu ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce wannan doka za ta yi aiki a wuraren ibada da wuraren hada-hadar kuɗi da wuraren biki da shaguna da makarantu da otel-otel da wuraren sayar da abinci da asibitoci da wuraren motsa jiki da sauransu.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan harin da aka kai a wata coci da ke garin Owo a jihar inda har mutum 40 suka rasu.

Advertisement

Haka kuma dokar ta buƙaci wuraren taron jama’a da su ɗauki masu gadi waɗanda aka horas da za su rinƙa lura da shige da fice na wuraren.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending