Connect with us

News

An kama mutanen da suka ƙwaƙule idon yaro a Bauchi

Published

on

Daga Kabiru basiru fulatan

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutum uku wadanda ta ce sun kwakule idanun wani yaro mai shekara 16 da haihuwa domin yin layar bata a jihar Bauci

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Ahmed Wakil, cikin wata sanarwa ya ce cikin mutanen da suka kama har da wani boka, wanda ke amfani da sassan jikin dan Adam domin yin tsafi da su.

Cikin wata tattaunawa da BBC ta yi da kakakin rundunar ya sanar da ita cewa ranar Jumma’ar da ta gabata a Yelwan Bauchi, wani mutum mai shekara 32 da haihuwa ya hada baki da wasu mutum biyu, daya mai shekara 38 da kuma wani boka mai shekara 52 da haihuwa, inda suka kai yaudari yaron zuwa wani jeji da ke kusa da cewa za su ba shi aiki a wata gona.

Advertisement

Bayan sun isa dajin ne sai suka shake yaron da waya har sai da ya suma, kuma daga nan suka kwakule idanun yaron biyu da wata wuka.

Cikin binciken da ta gabatar a cikin gidan mutumin da ta ke tuhuma, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano idanun yaron biyu cikin wata kwarya, da wata jaka cike da maganin gargajiya, da kuma wayar da aka shake yaron da ita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending