Connect with us

News

Tinubu ya tafi Faransa

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa domin gudanar da wasu ayyuka, kamar yada wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ke cewa.

Advertisement

Tunde ya ce ɗan takarar kuma jagoran jam’iyya mai mulki ba zai jima sosai ba a ziyarar da ya kai birnin Paris.

Kafin ya yi balaguron sai da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.

Advertisement

Sai dai wasu rahotanni da aka fitar a wasu kafofi na cewa Bola Tinubu ya je Faransa ne domin ya duba lafiyarsa.

A ranar 8 ga watan Yuni, Asiwaji Tinubu ya lashe tikitin takara a APC a zaben fitar da gwani.

Advertisement

Zai fafata da mutane da dama a zaben 2023 da ke tafe ciki harda ɗan takara daga babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar da kuma na sabuwar jam’iyya ta NNPP, Rabiu Kwankwaso.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending