News
An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allurar guba kan wasu mutane a Filato
Daga kabiru basiru fulatan
Babbar kotun jihar Filato ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma allurar guba kan wasu mutane guda uku a yau Alhamis.
Harin Sojoji Ta Sama Ya Kashe ’Yan Ta’adda 82 A Zamfara
Kotun ta Mai Shari’ah Arum Ashom da ke zamanta a birnin Jos ta yanke wa mutanen uku hukuncin kisa ne bayan ta same su da laifin suko wa Joseph Gonsum wuka a shekara ta 2015.
Babbar kotun Mai Shari’ah Arum Ashom ta ce ta samu Terry Kefas da Samson James da kuma Patrick Nyam da laifin hada baki don tafka aika-aikar da za ta iya kai wa ga mutuwar wani ranar 25 ga watan Disamban 2015 a unguwar Gada Biu cikin karamar hukumar Jos ta Arewa.
Haka zalika kotun ta ce ta samu mutanen uku da laifin kashe Joseph Gonsum ta hanyar caka masa wuka a ciki da sanin cewa mutuwa na iya kasancewa sakamakon aikinsu.
Rahotanni sun ambato lauya mai gabatar da kara, Barister John Ishaku Mantu yana yabawa wannan hukunci da ya ce hukuma ta yi ta bin kadinsa tun 2015.
Ya ce mutum hudu aka yi kara amma sai ɗayan Emmanuel Ujah ya riga mu gidan gaskiya a lokacin shariar.
Mai shigar da karar ya ce shari’ar ta samu jinkiri ne saboda tsarabe-tsarabe da lauyoyin wadanda aka tuhuma suka yi ta kawowa, baya ga tsaikon da annobar korona da yajin aikin kungiyar ma’aikatan kotu suka haddasa.
A nasa bangare, lauyan wadanda aka yi kara, Barister David Adudu ya ce ba su gamsu hukuncin na Mai Shari’ah Arum Ashom ba, don haka sun fara daukar matakan daukaka karar.
