Connect with us

News

RASHIN TSARO: Shugaban karamar hukuma zai raba wa ƙungiyoyin sa kai bindigogi 80 a jihar Filato

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

Shugaban karamar hukumar Wase a jihar Filato Ado Buba ya bayyana cewa gwamnatin sa zata siyo bindigogi domin raba wa kungiyoyin sa kai na karamar hukumar.

 

Advertisement

Buba ya ce zuwa yanzu ƙaramar hukumar ta siyo kuma ta raba wa kungiyoyin sa bindigogi kirar ‘pump action’ 80 a karamar hukumar.

Haƙƙin gyaran Arewa yana hannun al’ummarta ba wai shugabanninta ba-kabiru basiru fulatan 

Ya ce karamar hukumar na kokarin karo bindigogi domin kare rayuka da dukiyoyin mutane a karamar hukumar amma rashin kudi ya hana haka.

 

Buba ya ce gwamnatin sa ta siyo wadannan bindigogi ne ganin yadda rashi tsaro ya zama ruwan dare a karamar hukumar Wase.

 

Advertisement

Ya ce a dalilin rashin tsaro manoma da dama a karamar hukumar sa sun ƙasa zuwa gona a shekarar bara.

 

Buba ya ce samar da bindigogi wa kungiyar ‘yan sa kai zai taimaka wajen ganin bana manoma sun koma gona.

 

Hakzalika

 

Advertisement

APC ta gaza tunda har gwamna Matawallen Zamfara ya cewa mutane su mallaki bindugu don kare kawunansu.

 

Jam’iyyar PDP ta caccaki kungiyar APC a jihar Zamfara bayan da gwamna Matawalle yace mutane su sayi bindugu don kare kawunansu.

 

Sakataren PDP na jihar, Faruk Ahmad ne ya bayyana hakan inda yace hakan ya nuna cewa jam’iyyar APC ta gaza tunda har tace mutane su mallaki bindugu.

 

Advertisement

Inda kuma yace shi baya goyon bayan wannan shawarar saboda hakkin kare al’umma ya rataya ne akan gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending