News
Yau ake gudanar da taron ECOWAS a Ghana
Daga kabiru basiru fulatan
A yau Lahadi za a gudanar da taron koli na kasashen ƙungiyar ECOWAS a birnin Accra na Ghana.
Shugabannin ƙasashen za su tattauna kan batun sake ƙaƙaba wa ƙasashen Mali, da Burkina Faso da Guinea takunkumi kan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.
Haƙƙin gyaran Arewa yana hannun al’ummarta ba wai shugabanninta ba-kabiru basiru fulatan
Tuni ƙungiyar ta dakatar da su daga cikinta. Mali wadda ta fuskanci tashin hankali sama da shekara 10, ta fi ko wa jin jiki kan takunkumin tattalin arziki da ECOWAS ta sanya mata a watan Janairu lokacin taron kolin da aka yi.
Guinea da Burkina Faso kuwa an yi musu gargaɗi matukar suka gaza miƙa mulki salin-alin ga gwamnatin farar hula, to za su ɗanɗana kudarsu ta hanyar lafta musu takunkumi.
