Connect with us

News

Amfanin Ganyen ‘Aloe Vera’ Wajen Gyara Jiki

Published

on

Aloe Vera

Daga khadija Abdullah muhmd 

 

 

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul-sumul musamman ma a ce babu kuraje.

Wannan ganye na dauke da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sa fuska sheki da gyaran jiki da sauransu.

 

Advertisement

Jirgin dakon kaya maƙare da makamai ya yi hatsari a hanyar zuwa Bangladesh

 

Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da su wajen gyara fata da kuma gashin kai.

Ina so masu karatu su gane cewa, a duk lokacin da na lissafo abubuwan hadin kwalliya guda daya daga cikinsu nake so a yi amfani da shi.

Domin yawan sa wa fuska abubuwa da dama na haifar da fesowar kuraje.

Kodewar fuska: Yawan aiki ko shiga rana na sa fuska ta yi baki ko launinta ya zama biyu.
A samu ganyen ‘aloe vera’ a matse ruwansa sai a matsa ruwan lemon tsami a kwaba a rika shafawa a fuska don daidaita launin wannan fata.

Advertisement

Yaushin fata: Wannan ganye na rage tsufa a fuskar mutum. A matse ruwansa a hada da ruwan ‘rose’ a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.
Yawan gumi/ maiko: A samu ganyen a dan kankare bayansa, sannan a sa ruwa a tukunya a dora wuta sai ya dahu ya yi laushi, sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce, sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.
Gautsin fata: A markada dabino da gurji sai a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemon tsami, sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti 30 kafin a wanke.
Gyaran gashi: A matse ruwan ‘aloe vera’ a hada da man zaitun a kwaba su, su kwabu sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai. Yin haka na sa bakin gashi da kuma dada masa tsawo da karfi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending