Connect with us

News

Abinda ya sa muka hana zirga-zirgar Baburan Adaidaita Sahu cikin dare – Gwamnatin Kano

Published

on

Adaidaita Sahu

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta hana zirga-zirgar baburan Adaidaita Sahu ne bayan samun shawarwarin hukumomin tsaro kan aikata laifuka da suka yi kamari cikin dare.

Advertisement

 

 

Shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan ga jaridar ‘The Historica Nigeria‘ da yammacin Litinin.

 

Gwamnatin APC Ta Jefa Najeriya Cikin Tsaka Mai Wuya — Kwankwaso

 

Advertisement

 

Ya ce matakin ya zama wajibi duba da wasu nau’ukan laifuka da suka zama ruwan dare a jihar Kano, wanda ake yin su da hadin kan wasu masu baburan Adaidaita Sahun.

Baffa Babba Dan Agundi na cewa, magance matsalolin ya zama wajibi don ci gaba da wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Kano.

‘Shakka babu laifin kwacen waya ya zama ruwan dare, wanda kowa ya tabbatar da hakan, haka zalika akwai laifuka da dama da ake amfani da babur din Adaidaita Sahu wajen aikatawa, wanda Gwamnati ta dauki gabarar magancewa’, shugaban hukumar KAROTA.

Baffa Babba Dan Agundi ya kuma bukaci masu gudanar da sana’ar Adaidaita Sahu da su baiwa GWamnatin Kano hadin kai, wajen wanzar da dokoki nagari, da za su taimaka wajen ci gaban jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending