Connect with us

News

Shugaba Buhari ya samar da muhimman ayyuka 266 a Najeriya daga 2015 zuwa 2022

Published

on

Daga yasir sani Abdullahi

Femi Adesina ne ya bayyana hakan jim kadan, kafin fara zaman majalisar zartarwa gwamnatin tarayya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2022, ta kammala ayyuka akalla 266.

Advertisement

A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, Buhari ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wasu ayyuka 554 da gwamnatinsa ta gudanar, jim kadan kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya baje kolin ayyukan muhalli guda 266 da aka kammala a karkashin sa, ya umarci hukumomi da ma’aikatu da cewa sun taimaka wajen nasarorin da aka samu.

Advertisement

Buhari ya kuma bukaci jihohi da kananan hukumomi da su yi amfani da kason su na asusun kula da muhalli, musamman wajen gudanar da ayyukan da suka shafi muhalli wajen magance matsalolin muhalli a yankunansu.

Yayin da ya umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su ba da cikakkiyar sanarwa kan nasarorin da gwamnatin ta samu a wannan fanni, ya kuma bayyana cewa an amince da ayyukan da suka shafi muhalli guda 332 tun daga shekarar 2015, daga cikin 266 da aka kammala yayin da sauran 66 ke mataki daban-daban na kammalawa.

Advertisement

ADVERTISEMENT
Shugaban ya kuma yabawa sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da kwamitin gudanarwa na ofishin kula da muhalli, bisa yadda suka yi amfani da albarkatun da ake da su wajen aiwatar da ayyukan da aka amince da su yadda ya kamata, da kuma shirin bugawa.

Bugu da kari, Buhari ya umurci ma’aikatu da hukumomi da su baje kolin ayyukansu da nasarorin da suka samu ga jama’a ta hanyar wallafawa domin cin gajiyar ribar da gwamnati ke samu daga kokarin EPO.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending