Connect with us

News

Hisbah ta kama mota Hilux cike da giya a ɗaure cikin buhuna a Jigawa

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar mota, ƙirar Hilux, maƙare da giya, wacce aka ɗaɗɗaure a cikin buhuhuna.

Shugaban Hisbah a jihar, Malam Yusuf Lawan ya ce an kama motar ne a kan hanyar Kazaure zuwa Kano.

Advertisement

Ya ce jami’an Hisbah din ne da ke kan aikin sintiri su ka tayar da motar, inda ya ƙara da cewa da a ke binciken motar sai aka gano giya makare a cikin motar.

Lawan ya bayyana kamen a matsayin babbar nasara, inda ayabkaranda cewa giya barazana ce ga lafiya da kuma hankulan jama’a.

Shugaban ya roƙi jama’a da su taimaka wajen bayar da rahotonni ga hukumar domin ci gaba da maganace matsalar.

Dama gwamnatin Jigawa, karkashin shugabancin gwamna Badaru ta hana tare da rufe dukkan gidan mata masu zaman kansu tare da saida giya a fadin jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending