Connect with us

News

ISWAP Ta Kashe Mayakan Boko Haram 8 A Borno

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

A wani mummunan ɗauki ba daɗi da aka yi, ƙungiyar ISWAP ta kashe mayakan Boko Haram takwas a Jihar Borno.

Advertisement

Kwararren Manazarci kan Yaki da Tayar da Kayar Baya kuma mai fashin baki kan sha’anin tsaro a Yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama, ya ce lamarin ya faru ne a garin Jilli da ke tsakanin Kananan Hukumomin Gubio da Magumeri na Jihar Borno.

An ruwaito wani jami’in leken asiri yana shaida wa Zagazola Makama cewa, ISWAP ta yi wa mayakan na Boko Haram kwanton bauna ne a yunkurinsu na sace dabbobin mutanen yankin da ke Arewacin Borno.

DaKazalika, Zagazola ya ce baya ga kashe mayakan Boko Haram takwas da ISWAP ta yi, ta kuma samu nasarar kwace makamansu da babura.

A bayan nan dai ana zargin cewa yunwa ta addabi sansanonin kungiyar Boko Haram a yankin Bama a sakamakon karancin abinci.

Bayanai sun ce hakan ce ta sa mayakan ke kai hare-hare a kauyukan yankin da gonaki don samun kayan abinci, kudi, magunguna da sauransu.

A ranar 3 ga watan Yuli, an gano gawarwakin manoma uku a Gajeri, wani kauye mai tazara kadan da Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno, bayan wani hari da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai musu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending