Connect with us

News

Lauya Ya Maka Inec Kotu, Saboda Zargin Akwai Dungu Cikin Fam Ɗin Takarar Da Tinubu Ya Cike

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wani lauya mai Mike Enahiro-Egbah, ya maka Hukumar Zaɓe ta Ƙass kotu saboda ta ƙi ba shi cikakkun takardun bayanan da ke cikin fom na takarar shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya cike ba.

Advertisement

A Cikin kwafen ƙarar da lauyan ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Enahoro ya kai ƙarar hukumar zaben ce ita kaɗai, inda ya nemi kotu ta tilasta wa INEC ba shi dukkan bayanan da Bola Tinubu ya damƙa mata.

Mutane Su Tashi Su Kare Kansu Daga ’Yan Ta’adda – Sheikh Jingir

Advertisement

Yan sanda sun kama wanda ake nema ruwa a jallo, Rasheed Okoilu, a Osogbo

Lauyan, ya kuma bukaci hukumar zaben ta haɗa ma shi da dukkan kwafen takardun da Tinubu ya bada a lokacin zaɓen sa na Gwamnan jihar Legas cikin shekara ta 1999 da 2007.

Advertisement

Fom da bayanan da lauyan ke nema dai sun haɗa da katin shaidar rantsuwar da Tinubu ya taɓa yi, inda ya ce takardun makarantar sa sun ɓace, da ma duk wasu takardun bayanan da ya aika wa hukumar zabe.

Lauyan ya rubuta wa kotun cewa, ya aika wa hukumar zabe neman waɗannan bayanai tun a ranakun 13 da 22 Ga watan Yuli, kamar yadda Dokar Zaɓe ta Sashe na 29 (4) ta shekara ta 2022 da Sashe na 1 (1) da (3) da Sashe na 2 (6) da Sashe na 7 (4) na Dokar ‘Yancin Neman Bayanai ta tanadar.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

LIBRARY NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending