News
Mazauna garin funtuwa dakewayanta suna cigaba da samun barazana daga Yan bindiga
Daga Yasir sani Abdullahi
Mazauna garin Funtua da kewaye a Jihar Katsina dake arewa maso yammacin a Najeriya na kokawa game da yawaitar harin da ƴan bindiga ke kaiwa a yankin, waɗanda kuma suke satar mutane domin neman kudin fansa.
A cewar wasu daga cikin jama’ar yankin, tun ƴan bindiga suna musu ɗauki ɗai-ɗai, yanzu lamarin ya munana, kasancewar a ranar Alhamis ɗin da ta wuce kusan mutum goma aka kwashe a lokaci guda.
Mazauna kewayen birnin na Funtua sun bayyana cewa ƴan bindiga sun saka su a gaba inda suke kai masu hari suna garkuwa da mutane.
Jama’ar garin sun ce tun suna tsammanin samun sauki zuwa wani lokaci, lamarin sai ta’azzara yake yi har ta kai ga wasu ala tilas sun fice daga matsugunansu.
Wani mutum Dan funtuwa yace mazauna garin funtuwa dakewayan jahar suna ta tserawa daga mahallansu sabi da matsalolin Yan bindiga
Mutumin dai ya Kara dacewa wasu mutanan sabida barazanar da Yan bindiga suke musune yasa suka tarwatse wasu jahohin
