News
Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta sallami jami’inta saboda binciken wayar matafiyi
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumar ‘yan sandan Najeriya, reshen jihar Legas, ta sallami wani jami’inta, kofral Opeyemi Kadiri, saboda binciken lambar wayar wani matafiyi.
An sallami jami’in ne bayan da na’urar daukar bidiyo ta nuna shi yana binciken wayar mutumin a gefen hanya wanda kuma hakan ya sabawa umurnin da sufeto janar na kasar Usman Alkali Baba ya bayar.
A cikin bidiyon, an ji yo matafiyin na kokawa da nuna rashin amincewa kan bukatar da jami’in dan sandan ya yi na binciken wayarsa, inda ya ce sufeto ‘yan sandan kasar ya hana yin hakan, amma jami’in yaki saurara masa.
Kadiri dai na aiki ne da rundunar ‘yan sandan jihar Legas a shiyyar Dolphin.
Hukumar ‘yan sandan Najeriyar, ta gargadin jami’anta da cewa su tabbatar sun bi kwarewa da kuma yin abin da doka ya tanada yayin gudanar da ayyukansu, da kuma kiran jama’a na ganin sun bai wa ‘yan sandan hadin aiki yayin gudanar da aiki.
