Connect with us

Entertainment

Kungiyar 13×13 ta Mawakin Buhari, Rarara Ta Goyi Bayan Takarar Sha’aban Sharada

Published

on

Sha.aban

Daga Hamza Yusuf Abdulmumin

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kungiyar mawaka da jaruman masana’antar Kannywood ta 13×13 sun kammala shirin nuna goyan bayansu ga dan takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada.

Advertisement

Sha’aban Sharada dai ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar ADP inda ya samu tikitin takarar Gwamnan jihar Kano.

Wata majiya mai tushe dake kusa da Dan majalisar ta shaidawa jaridar Prime Time News cewa, kungiyar ta 13×13 wacce fitaccen mawakin shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta ta ziyarci

Advertisement

Sha’aban tare da nuna goyan bayansu ga takarar ta sa.

Majiyar ta ce “Jim kadan bayan ya ayyana shigarsa jam’iyyar ta ADP, kungiyar 13×13 ta kawo masa ziyara kuma sun aminta zasu yi tafiyarsa”.

Advertisement

Majiyar ta kara da cewa Rarara zai goyi bayan Sha’aban Sharada a matakin gwamna yayin da zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu a matakin kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending