News
Gwamna Zulum ya umarci yan sanda su garkame sakatariyar NNPP ta Borno
Daga: Muhammad Muhammad zahraddin
Ofishin yakin neman zaɓen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun zargi gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da bawa jami’an yan sanda umarnin rufe ofishin dake jihar ta Borno, tare da lalata musu wasu kayayyaki da kuma dukan wasu cikin ma’aikatan ofishin da magoya bayan su.
Jam’iyyar NNPP ta sanar da haka a safiyar yau, yayin wani taron manema labarai da ta kira, inda tace hakan na zuwa ne dai dai lokacin da ya rage kwanakin biyu da Sanata Kwankwaso zai ziyarci jihar domin bude ofishin, saboda haka suke kira ga gwamna da ya umarci jami’an yan sanda subar harabar sakatariyar tasu, domin hakan take hakkin su ne.
Kazalika jam’iyyar tayi kira ga jami’an tsaro da su guji hada kai da yan siyasa wajen musgunawa mutane, sannan tayi kira ga magoya baya da su kwantar da hankali, su tafi su cigaba da harkokinsu na yau da Kullum, sannan su cigaba da shirye-shiryen karbar bakuncin Kwankwaso nan da kwanaki biyu.
A bangare guda, kakakin hukumar yan sanda na jihar, Sani Kamil, yace a bashi lokaci domin yin cikakken bayani kan lamarin