News
#ShettimaChallenge: Da Gangan Na Sanya Kanbas Zuwa Taron Kungiyar Lauyoyi —Kashim Shettima
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar APC Sanata Kashim Shettima, ya ce da gayya ya yi shigar da ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, a taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), da aka gudanar a Legas.
Kashim Shettima da ya wakilci dan takarar shugaban kasa a APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce kafin taron, ya samu labarin cewa daya daga cikin ’yan takarar shugaban kasar Najeriya ya shirya masa manakisa.
Najeriya ta sakar wa kamfanonin sufurin jiragen sama na waje kuɗinsu da ta riƙe
Ta wani bidiyo da ya wallafa, Kashim ya ce “Na je Legas don taron NBA.
“Tawagata, ta samu labarin cewa daya daga cikin ’yan takarar shugaban kasa ya gudanar da tarukan kwanaki uku a jere, don shirya min manakisa.
“An gaya mini cewa cikin taron akwai makiyanmu, kuma kada ka manta ni ma’aikacin banki ne da ya samu horo daga daya daga cikin manyan ma’aikatan banki na duniya.
“Wannan ne dalilin da ya sanya na mayar musu da aniyarsu, da sanya wannan takalmin,. ” in ji shi.
A baya dai an karade kafafen sada zumunta hoton Kashim Shettima sanye da riga wando na Kwat, da takalmin Kanbas, abin da ya janyo masa tsokana daga matasa.
Baya ga haka fitattun ’yan wasan kwaikwayo da mawakan Najeriya irinsu Charly Boy, sun sanya wa wannan shiga ta tsokana taken #ShettimaChallenge a kafar sada zumuntan.
Wannan abu dai ya samu karbuwa a kafar, domin matasa da dama tuni suka fara sakin hotuna da bidiyon tsokana da irin shigar.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
