Sports
Da kyar idan Pogba zai buga gasar kofin duniya a Qatar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Za a yi wa dan wasan Faransa mai taka leda a Juventus, Paul Pogba tiyata a gwiwar kafarsa, watakila ba zai buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a bana ba kenan.
Pogba mai shekara 29 ya ji raunin a cikin watan Yuni, wanda kawo yanzu bai buga wasa ba tun fara kakar 2022/23.
Faransa za ta fara wasan kare kofinta, inda za ta kece raini da Australia ranar 22 ga watan Nuwambar 2022.
“A safiyar nan Pogba ya yi atisaye a karo na biyu, amma sai tsayawa ya yi, hakan ya sa muka yanke shawarar yi masa tiyata,” in ji kociyan Juventus Massimiliano Allegri.
Muna sa ran watakila ya dawo buga tamaula a cikin watan Janairu.”
Za a dakatar da wasannin Serie A daga ranar 13 ga watan Nuwamba domin buga kofin duniya, daga baya a ci gaba da fafatawa cikin Janairu.
An tambayi kociyan ko Pogba zai iya buga wa Faransa kofin duniya, Allegri ya kara da cewar ”Gasar kofin duniya ba matsala ta bace, kalubalen Juventus ya koma buga tamaula a cikin watan Janairu.”
Pogba ya sake komawa kungiyar da ke buga Serie A da taka leda a kakar nan, bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester United.
Dan wasan ya ci kwallo a karawar da Faransa ta doke Croatia 4-1 ta kuma lashe kofin duniya a Rasha a 2018 na biyu da ta dauka jumulla kenan
BBC NEWS
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days agoJami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
