News
Hukumar EFCC ta kama mutane bakwai da ake zargi da damfarar Intanet a Benin
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Jami’an hukumar EFCC reshen jihar Benin, a ranar Juma’a 9 ga watan Satumba, 2022 sun kama wasu mutane bakwai da ake zargi da damfarar yanar gizo a garin Benin, jihar Edo.
An kama wadanda ake zargin ne a maboyarsu, biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da zargin da ake yi musu na damfara ta intanet.
ICPC Ta Bayyana Yadda Tsohon Shugaban Sojoji Ya Wawure Naira Biliyan 4 , Ya Sayi Kadarori
Wadanda ake zargin dai su ne Akele Aisosa, Idemudia Lawson Osarodion, Daniel Chidube Emeka da kuma Ekoh Godswill.
Sauran sun hada da Junior Osagie, Idemudia Destiny Eghosa da Osaigbovo Lawrence.
Kayayyakin da aka samu a wurin kama su sun hada da: Mercedes Benz GLK 350 guda uku; daya Lexus RX 350; daya Mercedes Benz C400 AMG da iri daban-daban na waya
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
