News
Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ranar Asabar
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
A matsayin wani ɓangare na bikin samun ‘yancin-kai, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan ƙasar jawabi ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba.
Buhari zai gudanar da jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe yayin da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai daga Turawan Birtaniya.
Bam ya kashe Kwamishinan ‘yan sanda a Somalia
“Ana umartar gidajen talabijin da rediyo da sauran kafofin labarai na latironi da su jona jawabin daga gidan talabijin na NTA da kuma Rediyo Najeriya,” a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar.
Tun daga farkon makon nan aka ga sojojin Najeriya na shirye-shiryen bikin na ranar Asabar, inda jiragen soja za su dinga wasa a sama da kuma faretin girmamawa.
Advertisements
