Sports
Galatasaray na zawarcin Ronaldo, Kante na fuskantar rashin tabbas a Chelsea
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Galatasaray na son dauko ɗan wasan Portugal mai buga gaba Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, daga Manchester United a watan Janairu. (Fotomac – in Turkish)
Babban jami’i a Bayern Munich Oliver Kahn ya ce kungiyar Bundesliga na duba yiwuwar sayo Ronaldo a sabuwar kaka.(Bild, via Mail)
Abin Da Kasafin Buhari Na Karshe Zai Kunsa
Wolves na sa ran tattaunawa da Julen Lopetegui a wannan makon, bayan da Sevilla ta kore shi a matsayin koci. (Sky Sports)
Ɗan wasan tsakiya a Faransa N’Golo Kante, mai shekara 31, na ganin Chelsea ba ta son tsawaita zamansa a kungiyar, a daidai lokacin da kwantiraginsa ke shirin karewa a sabuwar kaka. (Footmercato – in French)
Arsenal ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan Porto da Iran mai shekara 30 mai buga gaba Mehdi Taremi. (A Bola, via TEAMtalk)
Real Madrid na farautar ɗan wasan Benfica mai shekara 18 asalin Portugal, Antonio Silva. (Calciomercato – in Italian)
Inter Milan na fatan cimma yarjejeniyar tsawo kan Calhanoglu bayan kungiyoyi ciki har da Everton sun gagara sayen ɗan wasan da ke buga tsakiya. (TEAMtalk)
Wani Attajirin Amurka Bill Foley, ya shiga tattaunawar cimma yarjejeniyar saye Bournemouth. (Athletic – subscription required)
Ana biyan ɗan wasan Norway Erling Haaland, mai shekara 22, £865,000-a kowanne mako a Manchester City. (Mail)
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya musanta rade-radin cewa zai bar Haaland ya tafi Real Madrid. (Mirror)
Mai rike da kofin Championship Sheffield United ta matsu ta saye ɗan wasan Scotland mai buga gaba Bobby Wales, mai shekara 17. (Football Insider)
Mataimakin shugaban kungiyar Barcelona ya gargadi kungiyar kan kudaden da ake kashewa, yana mai cewa ba za su dawo daidai ba sai sun rabu da wasu ‘yan wasa irinsu Gerard Pique, mai shekara 35 da Jordi Alba, ɗan shekara 33, da ɗan wasan tsakiya Sergio Busquets, mai shekara 34. (Mail)
Tsohon ɗan wasa Rio Ferdinand ya bukaci Manchester United ta saye ɗan wasan Borussia Dortmund asalin Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, da Real Madrid da Liverpool ke hari. (Mirror)
Kocin Leicester City Brendan Rodgers ya bayyana cewa ya yi watsi da tayin da aka gabatar masa har sau biyu na komawa wasu kungiyoyin. (LeicestershireLive)
