News
Wike ya naɗa sabbin mashawarta 14,000
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya naɗa mashawarta 14,000 ga bangarorin siyasa daban-daban a jihar.
Zan kawar da matsalar tsaro kafin na sauka daga mulki – Buhari
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri, ya sanyawa hannu, ta ce waɗanda a ka baiwa muƙaman za su taka rawar gani a harkokin gwamnati.
“Baya ga masu ba da shawara 14,000, Gwamna Wike ya kuma naɗa jami’an hulda da al’umma 319 da jami’an hulda da kananan hukumomi 40,” in ji Mista Ebiri.
“Nade-naden za su fara aiki nan-take”
Ana sa ran Gwamna Wike zai mika ragamar mulkin jihar a watan Mayun 2023 bayan cikar wa’adinsa na shekaru takwas.
Advertisements
