Connect with us

News

An sauke Ministan kuɗin Birtaniya daga muƙaminsa

Published

on

Kwasi Kwarteng

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Firaministar Burtaniya Liz Truss ta sauke ministan kuɗin ƙasar Kwasi Kwarteng daga muƙaminsa, makonni bayan naɗa shi.

Ana kallon wannan lamari a matsayin ɗaya daga cikin mataki mafi wahala da sabuwar firaministar ta ɗauka.

APC ta saduda, inda ta amince INEC ta buga sunan Machina a matsayin ɗan takarar sanatan Yobe-ta-Arewa

Wannan na nufin Kwarteng ya zama ministan kuɗi na biyu mafi ƙanƙantar wa’adi a kan matsayin, inda ya riƙe na tsawon kwana 38.

Korar Mr Kwateng ta ƙara tabbatar da shakkun da al’umma ke nunawa kan ƙaramin kasafin kuɗin da ministan ya gabatar.

Advertisement

Kasafin ya ƙunshi shirin zabtare haraji mai yawa da kuma ƙari a kuɗin da ƙasar za ta ranto.

Wani lamari da ya yi sanadiyyar faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, kasancewar ana faragabar shirin zai ingiza tashin farashi kaya, wanda yanzu haka yake a matsayi mafi muni cikin shekara 40.

Dama dai babban bankin ƙasar ya yi gargaɗin cewa za a yi fama da rashin tabbas a ɓangaren kuɗi na ƙasar sanadiyyar kasafin kuɗin.

A sanarwar da ya fitar bayan sallamar tasa, Kwateng ya ce zai ci gaba da mara wa Truss baya wajen aiwatar da manufofin gwamnatinta

BBC HAUSA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending