News
Rasha ta ce za a dauki tsawon watanni kafin sake gyara gadar Crimea da bam ya lalata
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Gwamnatin Rasha ta ce aikin sake gyara gadar Crimeazai dauki har zuwa nan da watan Yulin 2023.
Hukumomi sun ce harin bam ne ya lalata wani bangare na gadar a ranar Asabar da ta gabata, inda akalla mutum uku suka mutu.
Ambaliya na ci gaba da daidaita Australiya
Rasha dai ta zargi Ukraine da kai harin, sai dai, Kyiv bata ce ko ita ce ta kai harin ba zuwa yanzu.
Gadar mai tsawon mil 12, ita ce mafi tsawo a Turai, kuma ta kasance hanya da dakarun Rasha ke samun damar shiga Ukraine, inda a yanzu manyan motocin dakon kaya basa samun damar bi ta gadar.
Fashewar ta kuma janyo karyewar wani bangare na tsakiyar gadar da kuma lalata layin dogo.
An dai budewa jiragen kasa hanya wadanda suke bi ta gadar domin samun damar wucewa
