Connect with us

News

Ambaliya na ci gaba da daidaita Australiya

Published

on

Flood

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Akalla gidaje 500 ne ruwa ya tafi da su, sannan mutum daya kuma ya rasa ransa yayin da ambaliya ke ci gaba da daidaita Australiya.

 

Ambaliya a fadin Australiya ta kashe mutane sama da ashirin a wannan shekara.

Liverpool ne manyan abokan hamayyarmu in ji Guardiola

An bukaci al’ummomi a wasu jihohi uku na Australiya da su fice daga wurarensu yayin da mamakon ruwan sama ke janyo ambaliya a yankunan.

Advertisement

 

An yi ta samun ruwan sama mai karfin gaske a kasar a wannan shekara, inda wasu lokuta ake shafe sa’o’i 24 ana zuba ruwa.

 

Ambaliyar dai ta fi shafar jihar Victoria da ta kasance jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Australiya.

 

Ambaliyar ta kuma yashe hanyoyi tare da tilasta rufe makarantu da kuma katse wutar lantarki na gidaje da kasuwanni sama da 3,000.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending