Connect with us

News

NNPP ta nemi a binciki ɗan Ganduje, Abba, bisa zargin amfani da motocin gwamnati don yin kamfen

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Jam’iyyar adawa ta NNPP, ta bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin karkatar da dukiyar jiha da Abba Abdullahi Ganduje, ɗan gwamnan jihar Kano ya yi.

Advertisement

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Abba shi ne ɗan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar APC, a mazabar Dawakin Tofa, Rimingado.

Firayim Minista na Burtaniya, Liz Truss tayi murabus

Advertisement

A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar NNPP na jiha, Umar Doguwa ya fitar a yau Alhamis, jam’iyyar ta ce ta gano cewa gwamnatin jihar ta karkatar da motoci sama da 30 mallakar hukumar tattara kudaden shiga ta Kano, KIRS, domin gudanar da yakin neman zaben dan Gwamna Ganduje.

Motocin, a cewar Doguwa, wadanda ke dauke da hoton Abba Ganduje, ana shirin raba su ne ga shugabannin APC na mazabar Rimingado, Tofa, da Dawakin Tofa, domin yin gasa da dan takara Tijjani AbdulkadirJobe, wanda ya raba motoci kusan ashirin ga ƴan jam’iyyar NNPP kwanan nan.”

Advertisement

Doguwa, a cikin sanarwar, ya ci gaba da bayyana cewa, “motocin da ake zargi, an ajiye su ne a harabar jami’ar Maitama Sule ta Kano, ana jiran raba wa ga magoya bayan dan Ganduje, Abba.

Jam’iyyar adawar ta kuma yi Allah wadai da ajiye motocin a harabar jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke birnin a matsayin saba wa ka’idojin hukumar zabe ta kasa INEC na yakin neman zabe.

Advertisement

“Don haka muna rokon hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFFC, ICPC da INEC da su binciki almundahana da dukiyar kasa, bisa saba wa ka’idojin zabe.

Jam’iyyar ta kuma bukaci masu kada kuri’a a mazabar da abin ya shafa da kuma a fadin jihar da su yi watsi da siyasar son zuciya da cin hanci da rashawa da kuma abubuwan da ba su dace ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending