Connect with us

News

Ba Mu Da Tabbacin Ko Gwamnatin Nan Ta Cimma Burin Yan Najeriya – Aisha Buhari

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta ce saboda yawan tsammanin da ‘yan Najeriya ke yi ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba ta da tabbacin ko gwamnatin ta cika musu burin da suke da shi akanta.

 

Advertisement

Aisha ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi da BBC, inda ta ce hakan ne ya sa ta nemi afuwar ‘yan Najeriya.

Yan banga sun laƙada wa shugaban ‘yan jaridu na Jihar Zamfara duƙa

Advertisement

 

Rahotanni sun ruwaito Misis Aisha Buhari ta nemi gafarar ‘yan Najeriya game da wahalhalun da suke fuskanta yayin addu’o’i na musamman da ta shirya a ranar 1 ga watan Oktoba domin murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

Advertisement

 

Ta ce, “Abubuwan da ake sa rai a kanmu sun yi yawa kuma watakila bayan shekaru bakwai, ba mu cika tsammaninsu ba. Allah ne kaɗai ya san abin da ke cikin zuciyar wani.

Advertisement

 

“A matsayinka na dan adam, ba za ka iya cewa kana da gaskiya ko kuma ka yi abin da ya kamata ka yi ba, don haka gwamnati ta yi kokari sosai, gwamnati ta yi iya kokarinta amma ba za ta fi sauran ba. Don haka dole ne mu nemi afuwar ‘yan Nijeriya idan mun cimma burinsu ko a’a.”

Advertisement

 

Da aka tambaye ta wuraren da ta ke ganin gwamnati ta fi gazawa, Aisha ta ce ba ta bin shirye-shiryen gwamnati.

Advertisement

 

“Ban sani ba, domin ina gudanar da ofishina ne kamar sadaka; Ina karɓar mutane kawai, amma ba na cikin siyasa. Abin da nake yi shi ne tallafa musu ta fuskar lafiya ko ilimi. Ba na bin abin da suke yi, ”in ji ta.

Advertisement

 

A cewarta, jam’iyyar APC za ta lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

Advertisement

 

“Me yasa zaku min wannan tambayar? Mu (APC) za mu ci gaba. APC ce za ta ci zabe. Da yardar Allah.

Advertisement

 

Ta kara da cewa “Mun fuskanci babban kalubale domin lokacin da mijina ya hau mulki babu kayan aiki, amma na dage cewa mu ne muka ce za mu yi kuma dole ne mu yi.”

Advertisement

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Misis Buhari ta ci gaba da cewa ba ta da wani buri na siyasa.

Advertisement

 

Ta ce, “Na gode wa Allah da ya ba ni damar zama matar shugaban kasa. Matsayi ne mai girma. Ina rokon Allah Ya sa mu gama lafiya ya mika mulki ga gwamnatin APC.

Advertisement

 

“Ba ni da wani buri na siyasa. Zan zama matar tsohon shugaban kasa, me kuma nake nema?

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending