Connect with us

News

Yan banga sun laƙada wa shugaban ‘yan jaridu na Jihar Zamfara duƙa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Advertisement

 

‘Yan ɓangar siyasa sun lakawada shugaban ‘yan jarida na Jihar Zamfara, Comrade Ibrahim Musa Maizare duka, inda kuma suka yi barazana ga ‘yan jaridu a fadin jihar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ‘yan bangar sun yi ɗirar miƙiya zuwa ga shugaban ‘yan jaridun, sun umurci ma’aikata da ke aikin gyara wasu shaguna na kungiyar a sakatariyarta na jiha da su daina aikin gyara shagon wanda ake son amayar da shi a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe.

Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta

Advertisement

Ɓata garin sun ce ɓa za su ɓar wajen ba saboda wani dan siyasa ya basu, kuma muddin yana raye ba za su bar wurin ba.

Tun da farko an karɓi hayar shagon ne domin ɓude wajen sayar da abinci, sai dai, bayan wanda suka kama shagon sun fice, ‘yan ɓanga sun mayar da shi zuwa ofishin ƴakin neman zaɓe, inda a 2021, wasu ‘yan ɓanga na daban suka ƙona shagon.

Advertisement

Duk da zuwan jami’an tsaro sakatariyar ‘yan jaridun, ‘yan ɓangar sun ci gaba da zage-zage kan shugabanni da kuma sauran mambobin ƙungiƴar ‘yan jaridun na jihar Zamfara.

Da yake magana jim kadan bayan faruwar lamarin, Sakataren kungiyar, Ibrahim Ahmad Gada, ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun kare rayuka da ma dukiyoyin ‘yan jarida a jihar saboda rayuwarsu na cikin ɓarazana a yanzu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending