Connect with us

News

Shugaban China ya yi tazarce zuwa wa’adin mulki na uku

Published

on

Xi Jinping

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Shugaban China Xi Jinping ya kafa tarihi a matsayin Shugaban China bayan ya samu damar yin tazarce zuwa wa’adi na uku a mulkinsa.

Hakan na nufin Mista Xi ya zama shugaba mafi karfin fada-a-ji tun da Mao Zedong ya mulki kasar.

Tinubu ya buɗe ofishin kamfen a Kano

A halin yanzu dai Jam’iyyar Kwaminisanci ta ƙasar ta tabbatar da shi a matsayin babban sakataren jam’iyyar wanda hakan ke nufin a watan Maris mai zuwa yana da tabbacin ɗorawa a kan mulkin ƙasar na wasu shekaru biyar.

Kafin a kawo wannan matakin, tuni manyan kusoshin jam’iyyar suka bayyana goyon bayansu ga tsawaita wa’adin mulkin Mista Xi, baya ga amincewa da suka yi ga wasu sauye-sauye masu yawa da suka tilasta wa wasu manyan jami’ai ajiye mukamansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending