Connect with us

News

Kotu ta soke zaɓukan fitar da gwanin APC a jihar Rivers .

Published

on

APC

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal babban birnin jihar Ribas ya soke zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a faɗin jihar, sakamakon cire sunayen wasu daga cikin deliget a zaɓukan fitar da gwanin da jam’iyyar ta gudanar.

 

Advertisement

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka shigar da ƙara, kan ƙorafin cire sunayensu a matsayin deliget

INEC ta saka ranar gudanar da zaɓuka a jihohin Bayelsa, da Imo, da Kogi

Advertisement

Kotun ta ce ta soke zaɓukan kuma duk mutanen da jam’iyyar ta zaɓa a lokacin zaɓen fitar da gwanin ba halastattun ‘yan takara ba ne.

 

Advertisement

A lokacin zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar, wasu ‘yan jam’iyyar sun yi zargin cewa an cire sunayensu daga jerin sunayen deliget na jam’iyyar, lamarin da ya sanya su gudanar da zanga-zanga a harabar sakatiyar jam’iyyar da ke birnin Fatakwal.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending