News
Sojoji sun tarwatsa masu zanga-zanga a Sudan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sojoji a Kasar Sudan sun watsa hayaki mai sa hawaye a ƙoƙarin hana dubban masu zanga zanga maci zuwa fadar shugaban kasa.
Likitoci sun ce mutum ɗaya ya mutu bayan da motar sojojin ta buge shi.
INEC ta saka ranar gudanar da zaɓuka a jihohin Bayelsa, da Imo, da Kogi
Ana boren ne a duka faɗin Sudan, domin tunawa da juyin mulkin da ya toshe kafar dawowa mulkin dimokradiyya.
Ana zanga-zanga kusan duk mako a Sudan, tun bayan da Shugaban rundunar sojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan ya kwace mulki.
Ana zargin sojojin da kashe sama da masu bore 118 a cikin shekara daya, kuma ƙwace mulkin da sojoji suka yi, ya sa ƙungiyoyin bayar da agaji sun yanke kai taimako zuwa ƙasar, duk da halin matsin tattalin arziki da ta ke ciki.
