Connect with us

News

Gwamnan Anambra ya soke haraji kan ƴan talla, masu tura kura da sauransu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi mi’ara-koma-baya da ya soke duk wani harajin da a ka sanya wa ƴan talla, masu tura kura da sauran masu sana’o’in hannu a jihar.

Advertisement

 

Gwamna Soludo ya ba da wannan umarni ne a lokacin da ya ke jawabi ga al’ummar Anambra a kashi na biyu na taron yin nazari a kan harkar kuɗaɗen shiga, wanda ya gudana a gidan gwamnati da ke Awka.

Advertisement

EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar Ahmad Idris

A cewar Soludo, ƴan talla, masu tura kura da makaneza ba za su biya haraji a jihar Anambra ba.

Advertisement

 

Gwamnan ya kuma ƙara jaddada cewa dole ne sakon ya shiga dukkan kasuwannin Anambra.

Advertisement

 

“Masu tura kura kada su biya ko sisi a jihar nan. Su ma masu makaneza da ke aiki a kan titi ya kamata su daina biyan kowane kuɗi ga kowa. Ƴan talla ma kada su biya wani kuɗaɗe. Ya kamata a daina tsangwamar waɗannan talakawa.

Advertisement

 

“Wannan sakon ga kungiyoyin Kasuwa ne. Idan aka same su da wata shaida, za a rushe wannan ƙungiyar tare da gaggawa.

Advertisement

 

“Mu na son gina al’umma da talakawa ke jin an basu karfin gwiwa sannan kuma masu hannu da shuni za su samu karin albarkatu don samar da arziki da aikin yi,” in ji Soludo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending