News
Ma’aikata sun rufe filin jirgin sama na Legas Filaye
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An soke tashin jiragen da aka shirya tashinsu yau da safe a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, sakamakon zanga-zangar ma’aikatan filayen jiragen sama.
Lamarin ya sanya fasinjojin da suka yi sammako domin yin tafiye-tafiye cikin kunci.
Shugaban hukumar tace fina finai na jahar kano zai ankwance da tsohuwar Jarumar kannywood
Su dai ma’aikatan filayen jiragen sama na zanga-zangar ne saboda korar wasu daga cikin mambobin kungiyarsu 34 daga aiki, da kamfanin Bi-Courtney Aviation Services Limited (BASL) ya yi.
Kungiyar ma’aikatan sun yi zargin korar wasu daga cikin ma’aikatan nata da kamfanin ya yi ba ya bisa tsarin doka.
A wata sanarwa da kamfanin jirgin sama na Ibom Air, ya aikewa fasinjojinsa ya ce wannan zanga-zanga ta shafi zirga-zirgasa na yau a ciki da wajen Legas.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
