Connect with us

News

Ba za a iya kutse a na’urar tattara sakamakon zabe ba – INEC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan kasar cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na’urorin tattara sakamakon zabe ba.

 

Advertisement

Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin din Channels TV .

Rikicin APC Kano: Na San Wanda Ya Sa ’Yan Daba Su Kawo Min Hari —Doguw

Yana mai cewa ba za a iya yi wa na’urar kutse a ranar zabe ba.

 

”Ina so in sake tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa ba a yi wa na’urar kutse ba, za a kiyaye duka bayanan da ke cikin na’urar”.

 

Advertisement

“Bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na’urarmu, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na’urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su”, in ji shi

 

Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na’urorin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending