Connect with us

News

Yan Daba Sun Kona Ofishin INEC Na Ogun

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wasu ’yan daba da ba a gano su wane ba, sun kona muhimman kayyakin zabe a Ofishin Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Jihar Ogun.

 

Advertisement

Shaidu sun bayyana cewa wasu mahara takwas ne suka haura katanga suka shiga harabar suka cinna wa ofishin wuta da wasu katifun da suka jika da man fetur.

KAROTA:Dan’agundi ya amince da rushe wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Kundila.

Advertisement

Wani mai gadin ofishin da ke Abekuta babban birnin jihar, Azeez Hamzat, ne ya kira ’yan sanda da misalin karfe 1:00 na dare ya sanar da su faruwar lamarin.

 

Advertisement

Aminiya ta gano yadda gobarar ta cinye dakin taro da na rajistar baki na ofishin, kafin motar kashe gobara ta samu nasarar shawo kan wutar.

 

Advertisement

Rahotanni dai na nuna wasu kayyakin zabe masu muhimmanci ma sun kone sanadiyar gobarar.

 

Advertisement

Aminiya ta tuntubi Shugaban INEC na jihar, Niyi Ijalaye, ya kuma tabatar mana da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan sanda na ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata ta’asar.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending