News
Hatsarin mota ya ƙona mutum 11 ƙurmus a Jihar Kogi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani tsohon hoto da ke nuna haɗari a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a watan SatumbaImage caption: Wani tsohon hoto da ke nuna haɗari a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a watan Satumba
Mutum 11 sun ƙone ƙurmus a mummunan haɗarin mota da ya ritsa da ababe hawa daban-daban a yankin Ochadamu na Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
An Kai Hari 47 Kan Ofisoshin INEC A Shekara 3
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta faɗa cikin wata sanarwa ranar Alhamis cewa hatsarin ya ritsa da ababen hawa 20.
Jami’in hulɗa da jama’a na FRSC, Bisi Kazeem, ya ce za a iya kare afkuwar haɗurran, yana mai kira ga masu ababen hawa da su dinga kula da abin hawan nasu akai-akai.
“Tawagar bincike ta ba da rahoton cewa lamarin ya ritsa da mutum 18,” in ji shi.
“Daga cikinsu, mutum bakwai – uku maza huɗu mata – sun ji raunuka daban-daban – yayin da sauran 11 ɗin waɗanda ba a iya tantance jinsinsu ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton suka ƙone ƙurmus.”
Ya ƙara da cewa rahoton ya bayyana dalilin faruwar hatsarin da lalacewar titi, da shanyewar birki, da rashin ingancin abin hawa.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
