News
Mun saka Ido Sosai kan labaran karya da kamfanin Twitter ke fitar wa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayyar Nigeria tace tana saka Ido kan katafaren kamfanin Twitter kan labaran kanzan kuregen dake fitar wa bayan sauyin siyan da hamshagin dan kasuwarnan Elon musk yayi
A jiya Alhamis ne Ministan yada labarai,da raya Al,adu na nigeria Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana matsayin gwamnatin su a kan wannan batu a wani taron manema lanbarai a Abuja.
Muryar amurka ta rawai to cewa Ministan ya ce rufe dandalin sadarwar a bara ga masu amfani da shi ya biyo bayan yunkurin da wasu bata gari suke yi na haddasa tashin hankali a Najeriya da labaran kanzon kurege da yada bayanan karya da na kiyayayya
Hatsarin mota ya ƙona mutum 11 ƙurmus a Jihar Kogi
Lio ya yi gargadi cewa gwamnati bata da niyar hana duk wata kafar sadarwa gudanar da ayyukanta, amma kuma hakan ba zai sa ta kyale a yi amfani da wani dandalin sadarwa a jefa kasar cikin rikici da bala’i ba
Ministan ya ce: “Mutane da dama sun yi waya suna tambayarmu ko me zai kasance yarjejeniyar mu da Twitter saboda sauyin mallakarsa.”
“Wasu da dama kuma sun nemi jin martanin mu bayan rahotannin da ke nuna cewa an samu karuwar labaran kanzon kurege, da yada bayanan karya da kuma kalaman nuna kiyayya tun lokacin da shahararren dandalin sadarwa ya sauya ikon mallakarsa.”
Ya kara da cewa, “wasu mutane da yawa ma sun tambaye mu ko zamu sake hana Twitter aiki?.
Ya bayyana cewa, gwamnati tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter, kuma ko kadan, ba nufinta bane ta haramta duk wani dandalin sada zumunta ba ko kuma murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki.
A cewar Muhammed duk abin dake faruwa yanzu a shafin Twitter sananne ne ga kowa. Twitter ya zama dandalin zabi ga masu son tada zaune tsaye a Najeriya, ta hanyar yin amfani da labaran karya, da kalaman kiyayya.
Ya kara da cewa, babu wata al’umma da za ta kyale wani dandalin sada zumunta ya jefa ta cikin rudani. Tabbas ba Najeria ba
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
