Connect with us

News

2023: Ba Gudu Babu Ja Da Baya Kan Bada Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo – INEC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da ikirarin cewa ta na shirin yin watsi da watsa sakamakon zabe ta yanar gizo (PUs) tare da sauyawa zuwa tashar hukumar INEC wajen sanar da sakamakon zabe (IReV).

Advertisement

 

Daily trust ta rawaito cewa Kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja.

Advertisement

 

ASUU: Sanata Ndume ya ba da shawarar a zabtare albashin ‘yan majalisa a biya malaman Jami’a

Advertisement

 

A cewarsa, rahotannin da aka samu a wani sashe na kafafen yada labarai cewa INEC na son yin magudi a babban zaben 2023 ta hanyar yin watsi da shigar da sakamakon PUs kai tsaye da kuma na zahiri zuwa tashar IReV ta Registration Area Technical Support Staff (RATECHSS) wato rijistar ma’aikata don tallafin fasaha karya ne a zahiri.

Advertisement

 

“Hukumar ta sha tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta mika sakamakon zabe kai tsaye daga rumfunan zabe kamar yadda muka shaida a zabukan gwamnonin jihohin Ekiti da Osun da kuma wasu mazabu 103 da aka gudanar da zabukan gwamnoni da na kananan hukumomin birnin tarayya FCT da na kananan hukumomi tun watan Agustan 2020. Har yanzu ana iya duba sakamakon akan shafin.

Advertisement

 

“IReV na daya daga cikin sabbin abubuwan da Hukumar ta bullo da su don tabbatar da gaskiya da amincin sakamakon zabe a Najeriya. Don haka ba za a yi la’akari da cewa Hukumar za ta juya baya ta yi wa nata abubuwan kirkire-kirkire ba.

Advertisement

 

“An shawarci jama’a da su yi watsi da rahotannin. Na’urar tantamce sakamakon zabe (BVAS) da IReV sun zo ne don tabbatar da masu jefa ƙuri’a da kuma shigar da sakamakon zabe tun a rumfunan zaɓe a ainihin lokacin a Najeriya, “in ji Okoye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending