Connect with us

News

INEC za ta gana da Ganduje da jami’an tsaro  gabanin babban zaben 2023 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

A ranar Talata mai zuwa ne hukumar zabe mai zaman kanta za ta gana da gwamnoni da jami’an tsaro da wasu ‘yan takarar shugabancin kasa gabanin babban zaben 2023.

 

Advertisement

Wani zaman tattaunawa, wanda aka shirya a Nicon Luxury, Abuja, zai kasance kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye; Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; takwaransa na Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Benue, Samuel Ortom; da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, da zasu halarta.

Majalisar Dattijai za Bincika kan zargin karkatar da bashin rabin tiriliyan da bankin Raya Kasa (DBN) ya yi.

Sauran sun hada da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance, Hamza Al-Mustapha; Shugaban Majalisar Shawarar Jam’iyyu, Yabagi Sani; Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe.

 

 

Shugaban shirin Edwin Olofu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba.

 

Advertisement

Olofu, wanda kuma shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Post Platinum, ya bayyana cewa mahalarta taron za su yi muhawara kan yadda kasar za ta iya samun sahihin zabe ba tare da tashin hankali ba a shekara mai zuwa.

 

Sanarwar ta kuma ce, Al-Mustaphawould ya gabatar da jawabi mai taken, ‘Kalubalan Tsaro na Zamani da Tasirinsa a Zaben 2023.

 

 

Punch

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending