Connect with us

News

Mai Alkawarin Azurta ’Yan Najeriya 100m Ya Talauta 133m —Shehu Sani

Published

on

SANATA Shehu Sani

 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sanata Shehu Sani ya goranta wa Gwamnatin Shugaba Buhari kan ’yan Najeriya miliyan 133 da ke fama da fatata, duk da alkawarin ta na fitar da ’yan kasar miliyan 100 daga kangin talauci.

 

Advertisement

A sakonsa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce maimakon arzuta ’yan kasa gwamnati ta buge da jefa miliyan 133 daga cikinsu a kangin talauci.

 

Advertisement

Aisha Buhari Ta Yi Kunshi Mai Tambarin Tinubu

A cewarsa, “Sun yi alkawarin raba mutum miliyan 100 da talauci, sai ga shi a hukumance sun jefa mutum 133 ciki.”

 

Advertisement

A baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana tsare-tsaren da gwamnatinsa ta shirya don cire ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci ya zuwa 2030.

 

Advertisement

A watan Satumba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Kwadago da Raba Ayyuka, Kachollum Daju, ta fada wa manewa labarai cewa za a iya cimma wannan manufa muddin masu ruwa da tsaki suka yi aikinsu yadda ya kamata.

 

Advertisement

Sai dai kuma, a ranar Alhamis Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ba da sanarwar ’yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci, wanda shi ne kwatankwacin kashi 63 na yawan al’ummar kasar.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending