News
Hukumar Alhazai na gab da soma shirin aikin Hajjin 2023 a Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban hukumar Alhazai ta kasa a Najeriya, Zikrullah Kunle Hassan, ya ce a cikin watan Disamba za su fitar da adadin mutanen da za su je aikin hajjin baɗi a faɗin ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a wani taro kan shirye-shiren hajjin baɗi.
Mai Alkawarin Azurta ’Yan Najeriya 100m Ya Talauta 133m —Shehu Sani
Ya ce ba kamar bara ba da aka fuskancin jinkiri, a wannan lokaci hukumomin Saudiyya za su tuntubesu a kan lokacin domin ba su wadatacen lokacin shirye-shirye.
Ya kuma bayyana yadda matsalar bisa a wani lokaci ke zama kalubale ga shirye-shiryensu
Advertisements
