Politics
Tattakin Mutun Miliyon 1: Mun Gaya Masu Tamu Ba Irin Tasu Bace- Amb. Dandago
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ranar Lahadin Nan ne aka Gudanar da tattakin Mutun Miliyon daya domin nuna goyon bayan Kanawa ga takarar Asiwaju/Shettima da kuma Gawuna/Garo wanda aka gudanar a Kano, taron ya tabbatar da abinda Shugaban Jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje ke fadi, cewar “Tamu ba irin tasu bace”. Shugaban qungiyar Ganduje/Gawuna Ambasadas sannan Kuma kakakin Kungiyar Kasuwar Kantin Kwari Amb. Mansur Haruna Dandago ne ya bayyana haka alokacin da tattakin ya daura harami daga fadar Sarkin Kano zuwa Gidan Gwamnatin Kano sannan aka Wuce zuwa filin sukuwa.
“Muna Kara yiwa Allah godiya domin ya amsa Addu’ar da Gawuna keyi inda yake rokon Allah yasa muci zabe kafin ranar zabe. Wannan taron tattaki da aka tsara Mutane Miliyon daya a takaice ‘yar manuniya ta nuna cewa Kano ta Asiwaju/Shettima da Kuma Gawuna/Garo ce. Domin yadda Jama’a suka yi fitar dango ya nuna taron ya haura na Mutum Miliyon daya domin har lokacin da aka isa fadar Gwamnatin Kano, wasu basu ma samu tasowa daga fadar Sarkin ba saboda tsawon layi da dafifin Jama’a”. Inji Dandago
Da yake tsokaci Kan rukunin Jama’ar da aka hangi fusakunsu a wurin taron, Amb. Dandago cewa ya yi, ai wannan gayyar Khadimul Islam ce, saboda haka kowa ya bayyana, Jama’a sun amsa kiran Sarkin Tinubu Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kuma wani abin sha’awa tunda aka fara tattakin har zuwa karshen sa ko dan tsako bai ciwon kai ba. Saboda haka Jama’ar Kasa kowa yasha kuruminsa da yardar Allah APC daga sama har kasa Sak za’ayi.
Amb. Mansur Haruna Dandago ya jinjinawa kungiyoyi sama da 200 da suka halarci wannan gagarumin taro wanda ya tabbatar da irin Kaunar da Kanawa ke yiwa APC daga sama har kasa, sannan sai ya jinjinawa ‘yan Kwamitin da suka Jagorancin shirya wannan tattaki musamman Shugaban Hukumar KAROTA Alhaji Baffa. Babba Dan’agundi bisa namijin kokarin da suka nuna, hakan ya tabbatar da irin kyakkawan shirin da Kanawa suka shiryawa Zaɓen Shekara ta 2023..
