Politics
Jagaba Tinubu ya ziyarci Birnin-Gwari kafin fara yakin neman zabensa a Kaduna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jagaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Birnin-Gwari kafin fara yakin neman zabensa a Kaduna
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da tawagarsa sun isa jihar Kaduna inda za su gudanar da yakin neman zabensa a jihar ta Kaduna a ranar Talata.
Likitocin Da Suka Samu Horo A Kasashen Waje 439 Sun Fadi Jarabawar Gwaji
Tinubun ya samu rakiyar abokin takararsa Sanata Kashim Shettima da babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da na Kebbi, Atiku Bagudu sai kuma na Jigawa, Abubakar Badaru.
Gwamna Nasir El-Rufai da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar, Sanata Uba Sani da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna ne suka tarbe su a filin jirgin saman Dana dake Kaduna.
Bayan isowarsa jihar ta Kaduna, tsohon gwamnan na jihar Legas ya zarce jaje zuwa karamar hukumar Birnin Gwari, daya daga cikin kananan hukumomin da ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashin daji suka addaba don ya gane wa idanunsa halin da yankin yake ciki.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
