News
Buhari zai ƙaddamar da sabuwar takardar Naira a yau
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira da aka sake wa fasali a yau Laraba.
A watan jiya ne dai babban bankin Nijeriya, CBN, ya sanar da cewa zai sake fasalin Naira 1000, 500 da kuma 200 da ga ranar 15 ga watan Disamba.
Aikin bututun iskar gas na AKK zai haifar da habakar tattalin arziki, Inji Aminu Ado bayero
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata a wajen taron kwamitin tsare-tsaren kuɗi.
Emefele ya ce babban bankin ƙasa ba zai sauya ranar ƙarshe da ya saka na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankunan ƙasar domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.
Ya ƙara da cewa shugaban zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin a lokacin taron majalisar zartarwa na ƙasa.
Tun a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin ƙasar ya sanar da cewa za a ci gaba da kashe sabbin kuɗin tare da tsoffin kuɗin har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ƙudin.
