News
Ficewar da ƴan Najeriya ke yi zuwa ƙasashen waje ba laifi ba ne – Adesina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan yaɗa labaru, Femi Adesina ya ce ba matsala ba ce ficewar da ƙwararru ke yi daga ƙasar zuwa ƙasashen waje domin neman aiki.
Amnesty na kira da a saki ɗalibin da a ka kama bisa suka ga Aisha Buhari
Adesina ya bayyana haka ne lokacin wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels cikin ƙarshen mako.
Ya ce bai kamata a ɗora wa gwamnatin shugaba Buhari laifin ficewar da da matasan ƙasar ke yi zuwa wasu ƙasashe domin neman aikin yi ba.
A cewar sa matasan na ficewa daga ƙasar tun kafin zuwan gwamnatin shugaba Buhari.
Masana dai na nuna damuwa kan yadda ƙwararru daga Najeriya, kamar likitoci, da masana kimiyyar yaɗa labaru da sadarwa ke tafiya ƙasashen waje saboda matsi na tattalin arziƙi da ake fama da shi.
