News
Ƴan fashi sun kutsa coci daidai lokacin da ake ibada
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƴan fashi sun kutsa wani coci da ke birnin Johannesburg na Afirka ta kudu tare da yi wa masu ibada sata.
Ƴan fashin sun dakatar da huɗubar da ke gudana, sannan suka bi layi-layi suna karɓar kuɗi da kaya a hannun mutanen da ke cikin cocin, wadda ke a tsakiyar birnin.
Kyamarar tsaro ta cikin mujami’ar ta ɗauki lokacin da ƴan fashin suka dakatar da huɗuba.
Daga baya, cocin ya wallafa wani saƙo a ranar Lahadi, inda ya jajanta wa mutanen da abin ya rutsa da su, sannan ya buƙace su da su halarci wani zaman bayar da shawarwari da cocin ya shirya.
Kwamandan ƴan sandan na yankin ya yi Allah-wadai da lamarin, ya kuma shaida wa manema labaru cewar za a kamo waɗanda ake zargi.
-
Uncategorized7 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News6 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News2 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
