News
Jami’an DSS sun bai wa NNPC da IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen wahalar fetur
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bai wa kamfanin man NNPC da kungiyar dalilan man fetur ta IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su tabbatar da wadatuwar fetur a fadin kasar.
Kakakin DSS, Peter Afunanya, ne ya fitar da sanarwar a Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin fetur.
Mai ilimine Kadai zai,iya jogorancin karamar hukumar Dala…. bandirawo
Sanarwar ta ce NNPC ta tabbatar da cewa tana da wadataccen fetur jibge da zai wadatar da ‘yan kasar har bayan bukukuwa karshen shekara.
Ya ce an baza jami’an DSS a kowanne kusurwa na kasar domin hukunta duk maso boye mai ko yiwa harkar samar da mai zagon-kasa.
Sanarwar ta ce irin wannan matsala na fetur da ake haifarwa a kasar na taka rawa wajen sake asasa matsalolin tsaro.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
