News
Okupe ya ajiye aiki daga Darakta janar na kamfe din Peter Obi na Labour
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Doyin Okupe ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya matsa gefe daga aikin da ya ke yi.
Mista Okupe dai shi ne Darakta Janar na gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labour Mista Peter Obe.
Ya kuma sanar da cewa har yanzu ya na tare da Mista Obi, da bashi goyon baya akan tafiyar siyasar da ke yi.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wata Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ta yanke wa tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.
A wata sanarwa da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ta fitar ta ce Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wa Mista Okupe hukuncin a ranar Litinin bayan samun sa da laifin badaƙalar naira miliyan 702.
Sai dai kuma kotun ta bai wa Okupe zaɓin biyan tarar naira 500,000 kan
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
