News
2023: A ɗage zaɓe, idan ba haka ba zai zama ‘in conclusive’, Primate Ayodele ya faɗawa INEC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, a yau Juma’a ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC da ta dage ranakun gudanar da babban zaben domin kaucewa zaben da ba kammalalle ba.
Primate Ayodele ya bayyana cewa ba za a gudanar da zaben a wasu wuraren ba, inda ya ƙara da cewa ko da an yi shi a ranar da aka kayyade, to kuwa wasu za su yi masa zagon kasa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, Ayodele ya ce idan har INEC na son a gudanar da zaben cikin nasara, akwai bukatar a dage zaben domin su kara shirya wa.
Ya ce: ‘’Idan INEC ba ta dage babban zaben ba, ba za a gudanar da shi a wasu wuraren ba kuma zai kai ga zama ‘inconclusive’. Akwai wasu da za su yi wa zaben zagon kasa a wadancan wuraren,”
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
